Hukumar Kula Da Aikin Hajji Ta Kasa Zata Dauki Ma’aikata Na 2024

Advertisement

Assalamu alaikum jama’a barkanmu da wannab lokaci da fatan kuna cikin koshin lafiya.

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa wato National hajj commision zasu dauki sabin ma’aikata na wucen gadi a bangaren National Medical Team Na Hajj 2024.

Yadda Za’a cika.

Da farko Zaka Shiga Shafinsu

https://newsite.nigeriahajjcom.gov.ng/

Idan ya bude sai kayi download na GUARANTOR Form da kuma DECLARATION Form sai kayi Printout a wajen masu printing sannan ka cikesu

 • GUARANTOR Form: Zaka samu wani babban mutum wanda ya kai GL 12 a civil service ko kuma mai sarautar gargajiya ko alƙali wanda dole ya sanka a ƙalla tsawon shekara biyar, sannan dole ya zama yana da international passport
 • DECLARATION Form: kai za ka cike abinka ka saka hannu da date.

Bayan ka gama cikasu sai kayi scanning dinsu kokuma ka daukesu hoto a wayarka domin zakayi Upload dinsu idan kazo cikawa

Abubuwan da ake bukata wajen cikawa:

 • International passport
 • Passport (white background)
 • Valid Practising license
 • Professional certificate
 • NYSC certificate (where applicable)

Wadanda zasu iya cikawa

 • Doctors
 • Nurses
 • Pharmacists
 • Environmental Health Officers

Shekarun da ake bukata

 • Doctors and Pharmacists: 28 – 60years
 • Nurses and EHOs: 22 – 60 years
 • Waɗanda suka yi aikin NMT a shekara uku baya (2019, 2022 da 2023).

Yadda Zaka Nemi Aikin

Domin neman Aikin Danna Apply Now dake kasa

Apply Now

Bayan ya bude zai kawoka wajen da zakayi register saika shigar da bayananka, bayan ka gama Register sai kayi Login, username da passwors dinka.

Daga nan zai wuce dakai cikin shafin sai kaje ka cika sauran bayananka.

Abin Lura: Akin wannan shekaran volunteer service ne. ba za a biya kowa ba. amma dai za ka yi aikin hajji a kyauta. transportation, accommodation da abincinka duk nahcon ta ɗauke maka.

Za a rufe portal din ranar 26/02/2024.

Allah ya bada sa’a

Join Our Whatsapp Group